ZA’A FARA SHIRYA FINA-FINAN KURAME A JAHAR KANO – KSCB

Spread the love

Shugaban Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta jahar Kano Alh. Abba El-mustapha ya bayyana farin cikin sa tare da goyan bayan Hukumar tace fina-finai kan yadda za’a fara shirya fina-finan Kurame a jahar Kano.

El-mustapha ya bayyana hakan ne a jiya lokacin da KUNGIYAR KURAME MASU SHA’AWAR FARA SHIRYA FINA-FINAN TA KANO ta kawo masa ziyarar neman goyan baya a ofishin sa.

Abba El-mustapha ya jaddada aniyar gwamnatin Kano na tallafawa masu bukata ta musamman tare da basu tabbacin hada su da dukkan wani ake da tunanin zai’iya taimaka musu a ciki da wajen masana’antar kannywood.

Shima da yake jawabi, malam Rabi’u Aliyu Adam wanda shine jami’in Hulda da jama’a na Kungiyar ta Kurame cewa yayi hakika Kurame suma ya’yane kamar kowa a saboda haka suna da irin gudunmawar da zasu iya bayawa al’umma musamman masu bukata ta musamman.

Aliyu Adam yace manufar fara shirya fina-finan su shine samar da aiki ga
Kurame baya ga ilimantarwa tare da nishadantar da sauran masu bukata ta musamman.

Rabi’u Aliyu Adam ya kuma nemi goyan baya tare da tallafin gwamnatin Kano kan burin su na samar da fina-finan Kurame irinsa na farko a fadin Nigeria, a inda ya Kara da cewa tuni suka fara shirya wasu fina-finai da wayar hannu ta android.

A karshe Kungiyar ta godewa Shugaban Hukumar Abba El-mustapha tare da ma’aikatan sa dangane da lokacin da aka basu tare da shawarwari da zasu taimake su ta yadda suma zasu rinka cin gajiyar gwamnati kamar sauran yan Kungiyar kannywood.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *