Zabe: Gwamnatin Kano Ta Sanya Dokar Takaita Zirga-Zirga

Spread the love

Gwamnatin jihar Kano ta sanya dokar hana fita a fadin jihar , sakamakon Zaben kananan hukumomin da za a gudanar a ranar Asabar.

Kwamishinan Yada Labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Baba Halilu Dantiye ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce dokar zata fara aiki ne daga 12 na Daren Yau Juma’a zuwa 6 na yammacin gobe Asabar.

Sanarwar ta ce, daukar matakin ya biyo bayan tattaunawa da hukumomin tsaro, harma Gwamnatin ta yi fatan al’ummar za su bi wannan doka sau da kafa domin bada ta su gudunmawar wajen ganin an gudanar da zaben ba tare da wata matsala ba.

Dokar ta shafi dai-dai-kun mutanen dake zirga-zirga a kasa da kuma na ababen hawa a dukkan kananan hukumomin jihar 44 da kuma Mazabu 484.

Toh sai dai kuma wadanda dokar bata shafa ba sun hadar da ma’aikatan zaben, sauran masu aiki na musamman kamar Jami’an tsaro, Likitoci, ‘Yan Jarida da dangogin su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *