Zabe: Muhimmiyar sanarwa daga rundunar yan sandan Kano

Spread the love

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano na sanar da al’ummar Jihar kano cewa, Hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC zata sake gudanar da zabuka na kujerun Yan Majalisar Jihar Kano guda uku (3), Ranar Asabar 03/02/2024 a wadansu akwatinan zabe 66 na Kananan hukumomin Tsanyawa da Kunchi, Kura da Garun Mallam, da kuma kananan hukumomin Tofa da Rimin Gado.

2. Hukumar na bada tabbacin cewa tayi hadin kai da takwarorinta dake nan Kano domin tabbatar da anyi zabe lafiya an kuma gama lafiya, A don haka, al’umma su tabbata sun kiyaye da wadannan ka’idojin:-

i. Za’a takaita zirga-zirgar ababen hawa na Motoci, Kekunan Adaidaita Sahu da Babura tun daga daren jajiberin ranar zaben har a kammala a wadannan kananan Hukumomi Guda Shida (6) da za’ayi zabe, in banda motocin agaji, kamar Asibiti, Kashe Gobara, Ma’aikatan zabe, dadai sauran masu bada agaji na musamman bayan wadanda hukumar zaben ta tantance su.

ii. An hana duk wani jami’in dansanda rakiyar manyan baki (VIPs) ko masu rike da ofisoshin siyasa zuwa wuraren da ake gudanar da zabe.

iii. Ba a amince da duk wani nau’i na daba ko shigo da yan daba wajen garuruwan da ake gudanar da zabe ba, kuma za a baza Jami’an Tsaro domin kama masu kunnen kashi.

iv. Ba’a yarda duk wasu matasa yan tada zaune tsaye su kusanci inda ake gudanar da zaben ba.

v. Daukar duk wani makami ko kuma abun cutarwa a yayin gudanar da zaben, jami’an tsaro ba za su amince da haka ba.

vi. Iya wadanda suka cancanci zabe za’a bari a harabar gudanar da zaben.

vii. Duk wanda bashi da katin zabe da yake nuna lambar akwatin zabensa a wannan yanki, hukuma zatayi awon gaba dashi.

Yan Sanda Sun Kama Masu Buga Jabun Kudi 12 A Gombe

viii. Bamu aminta da kawo wani mutum ko wasu mutane inda ake zaben ba, Matukar ba hukumar INEC ce ta tantance suba. Don haka, iya wakilan Jam’iyyun da hukumar zabe ta tantance aka amince da zuwan su zaben.

ix. Za a kara fadada sintiri a wadannan kananan hukumomi da kuma saka matakan tsaro duk wuraren da ya kamata.

x. Ba a amince da hukumomin tsaro na gida ba a wannan zaben kamar su Hisbah, KAROTA, Vigilante da sauransu.

3. Rundunar ‘Yan sanda ta Jihar Kano na yiwa al’umma fatan yin zabe lafiya kuma a gama lafiya.

4. Don neman taimakon gaggawa ko kuma sanar da faruwar wani lamari, sai a kira wadannan lambobin 08032419754, 09029292926, 08123821575, ko ta manhajar “NPF Rescue Me” ko ta kafafen sadarwa kamar haka;

i. Facebook: Kano State Police Command
ii. Twitter: Kano State Police Command
iii. Instagram: Kano State Police Command
iv. Tiktok : Kano State Police Command.

Mungode da hadin kai da ake bamu

MAI SANARWA
CP MOHAMMED USAINI GUMEL, FIPMA, psc
KWAMISHINAN ‘YAN SANDAN JIHAR KANO

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *