Runduar ‘yansandan jihar Kano ta ce jami’anta sun fito domin tabbatar da tsaro a faɗin jihar.
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, a shafinsa na Facebook ya ce ”kamar yadda muka fito yau domin tabbatar da tsaro kamar yanda muka saba, muna rokon Allah (SWT) Ya cigaba kare al’ummar Jihar Kano da ƙasa baki ɗaya daga waɗanda ba sa son zaman lafiya”.
Tun da farko rundunar ‘yansandan jihar ta ce ba za ta bayar da tsaro a lokacin zaɓen ba bisa umarnin kotu, to amma Kiyawa ya ce za su fita aikin da suka saba na bayar da tsaro a faɗin jihar.