Zaben Cike Gurbi: Cikin Mutane 333 Da Muka Gurfanar Harda Mukarraban Gwamnati- CP Ibrahim Bakori

Spread the love

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta samu nasarar kama mutane 333 daga ranar juma’a 15 zuwa 16 ga watan Augustan 2025, tare da gurfanar da su a gaban kotuna mabambanta bisa zarginsu da tayar da tarzoma yayin gudanar da zaben cike gurbi a jihar.

Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan lokacin da yake yiwa manema labarai karin haske, a shelkwatar rundunar dake unguwar Bompai.

Ya ce gamayyar hukumomin tsaron jihar ne , suka samu nasarar dakile mafi yawan barazanar lokacin zaben cike gurbin, da aka gudanar a kananan hukumomin, Ghari/Tsanyawa da kuma Bagwai/Shanono.

CP Bakori ya kara da cewa sun kwato, Bindiga kirar Pump action 1, bindigu kirar gida 5, Gorori 94, Takobi 16, Adduna 18, Barandami 32, Wukake 18, Kwari da Baka 1, Kibiya 23, Dankuna 23, Duwatsu 45, Motoci 14, Takaddun kada kuri’a 163 , Akwatunan zabe 2 da kuma kudi naira miliyan hudu da dubu arba’in da takwas.

An gurfanar da su a gaban kotunan majistiri mai lamba 20 da 27 da 44 dake Nomansland da kuma mai lamba 8 da 53 a unguwar Gyadi-gyadi.

Kwamishinan ya ce sun gurfanar da su bisa zargin Hada kai da tayar da tarzoma da mallakar makamai masu hadari da tsoratarwa da ba tare da hujja ba a wuraren zabe da sata ko lalata kayan zabe da amfani motoci ba bisa ka’ida ba da kuma neman a zabe su a lokacin zabensu da dai sauransu.

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta ce ta yi kokari sosai domin ganin an yi adalci,saboda duk wanda aka samu laifin yiwa Damukuradiya zagon kasa za a hukunta shi.

Kazalika ya yabawa dukkan sauran hukumomin tsaro bisa jajircewa da sadukarwa da kuma nuna kwarewa, a lokacin zaben mai cike da kalubale, tare da dakile tashin hankali tare da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu.

A karshe ya yi kira ga al’ummar jihar Kano, da su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda tare da bawa jami’an tsaro hadin kai, har ya tabbatar da cewa tsaro bana gwamnati ba ne ita kadai aiki ne na kowa da kowa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *