Zabtarewar ƙasa ta kashe mutum 10 a yankin Amhara na ƙasar Habasha

Spread the love

Wata zabtarewar ƙasa da ta afku a yankin Amhara na ƙasar Habasha, ta yi sanadin mutuwar mutum 10 a gundumar Telemt da ke shiyyar Arewa ta Gonder, a cewar wani rahoto da kafar yaɗa labarai ta Amhara Media Corporation (AMC TV) ta bayar.

Zaftarewar ƙasar wadda ta afku a ranar 24 ga watan Agusta, ta kuma jikkata mutane 8 tare da raba mutum 480 da gidajensu da muhallansu.

Shugaban ofishin sadarwa na gwamnati a gundumar Telemt, Tesfaye Workneh ya tabbatar da cewa kawo yanzu an gano gawarwakin mutane huɗu.

zabtarewar ƙasar ta kuma yi sanadin asarar fiye da dabbobi 35 tare da lalata amfanin gona sama da hekta 30 na fili.

Wannan lamari dai ya biyo bayan zabtarewar ƙasar da aka yi a kudancin Habasha a watan Yuli, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum aƙalla 250.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *