Lauyan Nan Da Yake Zargin Kudinsa 950k Sun Bata A Motarsa Da Karota Suka Dauka Zai Nemi hakkinsa A Kotu Saboda Gaza Cimma Matsaya.

Spread the love

Lauyan nan da yake zargin wasu jami’an hukumar Karota ta jihar Kano, da dauke masa mota da kudinsa naira dubu 950k, Barista Ahmad Sani Bawa, ya bayyana cewa zai nemi hakkinsa a gaban kotu sakamakon rashin samun daidaito tsakaninsu da hukumar.

Tunda farko barista Ahmad Sani Bawa, ya shigar da korafinsa ta hannun lauyoyinsa , a ofishin kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, don gudanar da bincike kan lamarin.

A cewarsa ya ajiye motarsa kuma bai ajiye a wurin da bai kamata ba, amma lokacin da ya zo dauka sai ya tarar batanan, inda ya bincika  ya gano ta, a wani karamin ofishin hukumar Karota dake Kano.

Sai dai lokacin da yake son jin dalilin daukar motar tasa ba tare da an sanar dashi ba , ya zargi wani jami’an hukumar da cin zarafinsa ta hanyar duka.

Amma hukumar Karota ta jihar Kano ta musanta zargr-zargen tun a baya, inda kwamishinan yan sandan Kano, ya bayar da umarnin bincika lamarin ta hanayar gaiyato dukkan bangarorin da lamarin ya  shafa.

Bayan tattaunawar ne a makon da ya gabata aka dauko motar lauyan daga hukumar Karota, zuwa hannun jami’an yan sandan Kano, sai dai an bude motar babu kudin da lauyan yake zargin an sace da kuma wani Agogo da darajar kudinsa ta haura naira miliyan uku.

Ahmad Bawa ya kara da cewa bai ga dalilin da jami’an hukumar za su dauke motarsa ba tare da sun ajiye wani da zai sanar dashi ba.

Ya kuma ce yin hakan zai sanya idan mutum yana da ciwon hawan jininsa zai iya tashi sakamakon damuwa daka iya zuwa lokaci daya.

Rundunar yan sandan jihar Kanon ta  ba su damar suje su sulhunta a tsakaninsu, amma idan hakan bata samu ba za su dawo don tafiya gaban kotu.

Sai dai zaman yin sulhun da aka yi, a hukumar Karota bai yiwuba saboda lauyoyin mai korafin sunce hukumar ta nemi a rubufe maganar baki a yi hakuri ba tare da an biya ko sisin kobo ba, inda su kuma suka ce abu ne da ba zai yiwuba, domin ba abunda ya rage musu illa su garzaya gaban kotu domin ita ce zata warware komai.

Barista Ahmad Sani Bawa, ya ce lauyoyinsa da kuma na hukumar Karota sun zauna don a fahimci ,kuma sun nemi Karota ta biya su naira miliyan biyar, da kudin da yake zargin sun bata a motarsa bayan an dauke ta da kuma na Agogon da ba a gani ba wanda kudinsa ya kai sama da naira miliyan uku.

Sai dai a yayin zaman lauyoyin Karota sun bukaci lauyoyin mai korafin ya yi hakuri abar magana ba tare da an biya ko sisin Kobo ba, inda lauyoyin mai korafin suka ce sam bata yiwuba.

‘’ kawai suna cewa ayi hakuri naje na dauki asara, amma zan bi hakki na, kuma ni banki yin sulhu don haka za kai kotu’’ Ahmad Sani Bawa.

A karshe sun ce yanzu damar su ta karshe ita ce tafiya kotu tunda ba a fahimci juna ba.

Mai magana da yawun hukumar Karota, Abubkar Ibrahim Sharada , ya bayyana cewa ba zai ce komai ba kan lamarin domin zaman da aka yi bai samu halatta ba, saboda wasu uzirrika kuma lauyansu hukumar an sauya masa wajen aiki zuwa majalissar dokokin Kano don haka ba zai ce ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *