Zamu ci gaba da bujuro da Abubuwan Alkhairi dan kyautata rayuwar masu bukata ta musamman a yankin Rakibu: Rurum

Spread the love

 

Wakilin Kananan Hukumomin Rano Kibiya da Bunkure a majalisar kasa *RT Hon Kabiru Alhassan Rurum* ya bada tallafin buhunan Shinkafa 25kg da kudi cefane naira dubu 10-10 ga masu bukata ta musamman na kananan hukumomin sa.

Da yake Jawabi ga nakasassun su 150, *Turakin Rano Wanda DG Alh Alhassan Abubakar Kibiya* ya wakilta yace duba da halin matsi da ake ciki a halin yanxu yasa yaga dacewar maida hankali kacocan wajen tallafawa rukunin Al’umma da kayan abinci da ‘Yan kudade domin a rage radadi.

Yace Masu bukata ta musamman na bukatar matukar kulawa bama ga masu mulki ba har da sauran Al’ummar gari duba da yadda rayuwa tayi tsada a yanxu, Kuma shi a nasa bangaren lokaci zuwa lokaci zai rinka waiwayar su don tallafa musu bawai sai sun rinka barace barace ba.

Ya Kuma yabawa Nakasassun bisa hakurin da suke nunawa da gudummuwar Addu’oi da suke masa a Koda yaushe.

Cike da farin ciki (wasu harda Kuka) mutanen mika godiya mara misaltuwa ga *RT Hon Kabiru Alhassan Rurum* daya ke taimaka musu ko da yaushe Sun Kuma yi Addu’a ta musamman gareshi da fatan Allah ya cigaba da yi masa jagoranci ya daga likkafarsa ya kuma kiyayeshi daga sharrin makiya da mahassada da sauran fitintinun zamani..

*Fatihu Yusuf Bichi*
*Media Aide to Rurum*
*Jan 12th, 2025.*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *