Zamu gayyaci masu zuba hannun jari dan bunkasa tattalin arzikin masarautar Kaltungo da Jihar Gombe:sarkin Kaltungo

Spread the love

Daga Rabiu Sanusi

Mai martaba sarkin Kaltungo dake jihar Gombe Engr, Saleh Muhammad ya bayyana kudurin sa na gayyatar manyan yan kasuwa domin zuba hannun jari dan bunkasa tattalin arziki a karamar hukumar Kaltungo da jihar Gombe baki daya.

Sarkin wanda ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a lokacin gudanar da bikin kamun kifi da ya gudana a Kasar Kaltungo cikin makwan nan.

Engr. Saleh Muhammad wanda ya fara da yima mahalarta taron godiya da wadanda zasu shiga ruwan dan cigaba da daukaka wannan harka da murnar bikin Kamun kifin da ya gudana.

Yan Sanda Sun Fatattaki ‘Yan Bindiga A Abuja

Yan Kasuwa a Kano Sun Koka Kan Kama Kayansu da Hukumar Kwastom Keyi

Mai Kaltungo ya kuma bayyana cewa a yanzu yakamata ace sun samu tuntubar masu hannu da shunin da zasu iya zuwa dan saka hannun jarin su a wannan harkar da idan har sun yi abinda yakamata zata taimaki wannan masarauta da jihar su ta Gombe hadi da kasa baki daya.

Sarkin Kaltungo, ya.kara da cewa yana gargadin al’ummar sa dasu mai da hankali wajen kara adana kayan abincin su da suka noma,duba da irin yadda rayuwa tayi tsada musamman kan kayan masarufi.

“Haka zalika ina horon ku daku zama masu hadin kai,kada kusa ke wasu su shigo mu tare da samun damar far mana har su samu damar kawo mana rashin zaman lafiya a wannan gari da muke zaune lafiya.”

Mai kasar Kaltungon ya kuma bukatar jama’ar sa da su kara kaimi wajen kara hada kai da yima wannan yanki nasu addu’a da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Uban kasar ya jaddada kudurin sa na mai da wannan gurin kamun kifi wajen shakatawa na kasa da kasa bawai Kasar Kaltungo kadai ba ko jihar Gombe ta hanyar gayyato masu zuba hannun Jari kamar yadda ya shaida tun farko, kasancewar gurin na da yalwa.

“Muna kuma masu gargadin masu sare mana bishiyoyi a wannan kasa tamu dasu bari da kaucewa matsalar da zata iya faruwa, dan haka dole kowa ya zama Jakadan Kasar Kaltungo mai kuma san kawo cigaban karamar hukumar mu ta hanyar kishin abin da muke so.

Daga karshe ya kuma yima mahalarta taron fatan alkhairi tare da fatan zasu koma gida lafiya,wanda kuma ya kara yabawa da kokarin al’ummar sa da yima masu fatan nasara akan abinda suke yi ko ina suke, sannan yayima mai martaba sarkin Gombe da Gwamna Inuwa Yahaya fatan alkhairi bisa kokari da kulawa akan jihar Gombe baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *