Zan yi murabus idan na gaza kai ƙarshen binciken Yahaya Bello – Shugaban EFCC

Spread the love

Shugaban hukumar EFCC da ke yaƙi da masu yi wa arzikin Najeriya zagon ƙasa, Ola Olukoyede ya sha alwashin yin murabus idan na gaza gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

A wani taron tattaunawa da zaɓaɓɓun editoci a hedikwatar hukumar da ke Abuja, babban birnin Najeriya, shugaban hukumar ya yi alƙawarin hukunta duk masu kawo kawo tarnaƙi ga kama tsohon gwamnan.

A ranar 18 ga watan Afrilu, EFCC ta ayyana Bello a matsayin wanda take nema ruwa a jallo saboda zarginsa da badaƙalar kuɗi ta naira miliyan 80.

Yahaya Bello dai bai bayyana gaban kotu ba tun bayan ayyana ana nemansa ruwa a jallo.

Shugaban EFCC ya ce da kansa ya kira Bello cikin mutunci inda ya nemi da ya bayyana gaban hukumar ya kuma yi bayani kan tuhume-tuhumen da ake masa.

Shugaban EFCC ya ce duk da kiran wayar, tsohon gwamnan bai amsa gayyatar ba.

Yahaya Bello dai ya musanta gayyatar da aka yi masa inda ya ƙalubalanci EFCC ta gabatar da kwafin takardar gayyatar da ta aike masa.

Cikin wata sanarwa da ofishin yaɗa labaran tsohon gwamnan ya fitar, Yahaya Bello ya zargi EFCC da yaɗa jita-jita.

Shugaban EFCC ya ce “Idan har ban ga ƙarshen binciken da ake yi wa Yahaya Bello ba, zan ajiye aikina a matsayin shugaban EFCC.

“Na gurfanar da tsoffin gwamnoni biyu da a yanzu aka ba su beli – Willie Obiano da Abdulfatah Ahmed. Da mun bi Bello tun Janairu amma muka jira umarnin kotu.

“Idan har na iya gurfanar da Obiano da Abdulfatah Ahmed da Chief Olu Agunloye, me zai sa ba zan gurafanar da Yahaya Bello ba?

Olukoyode ya kuma ce tsohon gwamnan ya kwashi dala dubu 720 daga asusun gwamnati kafin barin mulki domin biyan biyan kuɗin makarantar ɗansa.

Tsohon gwamna Bello ya roƙi babbar kotun tarayya a Abuja da ta soke izinin kama shi da aka bai wa EFCC ranar 17 ga watan Afrilu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *