Dan majalissar tarayya Mai wakiltar al’ummar kananan hukumomin Kiru da Bebeji a jahar Kano, Hon. Abdumumin Jibrin Kofa, ya yaba wa rundunar yan sandan Kano, bisa namijin kokarin da ta ke yi na wanzar da zaman lafiya, a mazabarsa da kuma jahar baki daya.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da aka samu tashe-tashen hankula da wasu matasa suka yi cikin ma su Zanga- zangar Adawa da tsare-tsaren gwamnatin tarayya Wanda ya Sanya al’ummar kasar cikin kuncin talauci.
Sanarwar da kakakin rundunar yan sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar Lahadi , ta ce Dan majalissar tarayya Abdumumin Kofa, ya yaba da matakan da rundunar ta dauka wajen shawo kan lamarin tare da kwato kayayyakin da batagarin matasan suka sata.
Kofa ya bayyana hakan ne a wata ziyara da ya Kai wa kwamishinan yan sandan jahar Kano, CP Salman Dogo Garba, a ranar Lahadi.
Tun a ranar Alhamis din da ta gabata Ake zargin wasu batagari sun fake cikin ma su Zanga-zangar Neman yanci, Inda suka yi sace-sace da barnata kayan gwamnati da al’umma.
Da yake nasa jawabin kwamishinan yan sandan Kano CP Salman Dogo Garba, ya yaba da kwarin gwiwar da suka samu daga Hon. Abdumumin Kofa, ya kuma tabbatar ma sa cewa rundunar za ta ci gaba da jajircewa na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jahar Kano.
Idan ba a manta ba idongari.ng ta ruwaito mu ku cewa rundunar yan sandan jahar ta yi holen matasa 326 , a ranar juma’a bisa zarginsu da yin barna da kuma sata a ranar farko ta Zanga -zanga.