Zanga-zanga : Akwai Yiwuwar Biyan Matasan N-Power Hakkokinsu Kafin Watan Janairu

Spread the love

 

Kungiyar matasan da suka ci gajiyar Shirin N-Power, sun janye Zanga zangar da suka shirya gudanar wa daga yau Litinin zuwa ranar Juma’a 6 ga watan Disamba 2024.

Shugaban kungiyar na kasa Kwamared Muhammed Abubakar Habib (GMB), ne ya sanar da hakan, Inda ya ce sun dauki matakin janye Zanga zangar, ne sakamakon cimma matsaya da suka yi da Ministan ma’aikatar Jin Kai, Farfesa Nentawe Yilwada, a gidansa dake birnin tarayya Abuja.

Ya kara da cewa Ministan ya tabbatar da cewa za su duk mai yiwuwa wajen biyan su hakkokin da suke bin Gwamnatin tarayya, Kafin watan Janairu na sabuwar shekarar 2025.

Wannan dai na Zuwa ne bayan shiga tsakani da Yan majalissar Dattawa , da kuma barista Adeyanju Deji, suka yi don biyan matasan bashin da suke bi.

Sai dai kungiyar matasan N-Power, sun ce za su jira don har sai sunga matakin da Ministan zai dauka.

Muhammed Abubakar Habib, ya ce sun aike wa hukumomin tsaro, janye Zanga zangar da suka shirya gudanar wa.

Tsohon shugaban kasa Muhammed Buhari , ne ya fito da Shirin N-Power a shekarar 2016, don tallafawa matasa wajen Samun abun dogaro da Kai, sai dai an samu kalubale na rashin biyan wasu dada cikin matasan hakkokinsu.

A karshe kungiyar ta godewa hukumomin tsaro, Ministan Jin Kai, Barista Deji Adeyanju da kuma kafofin yada labarai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *