Zanga-Zanga: Bata-gari sun sace takardun shari’ar Ganduje a Kano

Spread the love

Gwamnatin Kano ta bayyana cewa bata-gari sun sace takardun shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje kan tuhume-tuhumen da suka shafi rashawa da almundahanar kudin al’umma.

Aminiya ta ruwaito yadda wasu bata-gari suka yi ta’adi a Babbar Kotun Jihar Kano da ke harabar Sakatariyar Audu Bako yayin zanga-zangar tsadar rayuwa da ta rikide zuwa tarzoma.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a yammacin wannan Larabar, Gwamnan ya bayyana damuwa dangane da lamarin yayin da kai ziyarar gani da ido kan irin ta’asar da bata-garin suka yi a Babbar Kotun.

“Abin takaici ne matuka yadda makiyan Jihar Kano suka dauki hayar wasu bata-gari suka lalata daya daga cikin gine-ginen jama’a masu dimbin tarihi da nufin dakile tuhumar da ake yi wa Shugaban Jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Dokta Abdullahi Umar Ganduje da iyalansa da hadimansa,” inji sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa bata-garin sun lalata kusan dukkanin sassan Babbar Kotun da suka hada da ofishin Alkalin Alkalan jihar, lamarin da ya janyo asarar sama da Naira biliyan daya ta hanyar satar kayan ofis, lalata ofisoshi, kona motoci da sauran abubuwa.

Sanarwar ta kuma ambato gwamnan na cewa ta’asar da bata-garin suka yi kulallen lamari ne ca aka kitsa da gayya domin sace takardun tuhume-tuhumen da ake yi wa tsohon gwamnan jihar kan zargin rashawa.

Gwamnan ya bayar da umarnin fara gyaran kotun nan take, inda kuma ya yi wa Babbar Alkaliyar Kano, Dije Aboki da manyan alkalan kotun jaje bisa wannan ibtila’in da ya afkawa kotun.

Gwamnan wanda ya nanata cewa bangaren shari’a shi ne ginshikin da ke share hawayen duk wani mara gata, ya kuma ba da umarnin a gaggauta soma gyare-gyaren ginin kotun da kuma tanadar karin jami’an tsaro ba tare da bata lokaci ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *