Zanga-Zanga: Fadar shugaban kasa na yunkurin kama Peter Obi – inji mai magana da yawunsa

Spread the love

Ofishin yada labarai na tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP ya musanta zargin da mai magana da yawun fadar shugaban kasa, Bayo Onanuga yayi na cewa magoya bayan Obi ne ke shirya gudanar da zanga zanga a fadin kasar nan.

Ofishin ya bayyana zargin a matsayin mara tushe, inda ya ce fadar shugaban kasa na shirin amfani da zanga zangar wajen kama Peter Obi.

A wani sako da ya wallafa a shafin X a ranar Asabar, hadimin shugaban kasa Tinubu, Onanuga yayi ikirarin cewa magoya bayan Obi ne ke shirya zanga zangar adawa da gwamnatin Tinubu.

Ya ce za a dora alhakin duk wani tashin hankali da ya faru a zanga zangar kan Peter Obi.

Sai dai a sanarwar da ofishin yada labarai na Peter Obi ya fitar wacce ke dauke da sa hannun Yunusa Tanko ya ce an kirkiro da zargin ne domin kama Obi.

Ya ce tsohon Gwamnan na Anambra bai taba goyan bayan tada hargitsi ba.

Kakaki24

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *