Ana zanga-zanga kan yawan kashe mata a Kenya

Spread the love

Ana zanga-zanga a biranen Kenya saboda yawan kashe mata da kuma cin zarafinsu a ƙasar.

Hakan ya biyo wani kisa da aka yi wa mata da dama a baya-bayan nan.

Daruruwan mutane ne suka taru, yayin da wasu ke ɗauke da kwalaye masu rubuce da sunayen wadanda aka kashe.

Hukumar tsaron Civil Defence ta cafke matasa 2 bisa zargin fasa shago da satar buhunan Zobo 10 a Jigawa

Kungiyar Amnesty ta ce sama da mata 500 aka kashe a Kenya tsakanin 2016 zuwa 2023.

Akasarin matan mazajensu ko makusanta ke hallakasu. Kungiyar na son mahukunta sun yi adalci wajen bin kadin duk wani salon cin zarafi da wariya da ake nunawa mata a kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *