Kungiyar mata lauyoyi (Women Lawyers Congress ) ta gudanar da wata zanga-zanga da ta dauki hankali akan titin Tukur Road da ke birnin Kano inda ta yi kira ga babban Sufeton yan sandan Nijeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, kar ya amsa kiran da gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi don a sauya masa kwamishinan yan sandan jihar Kano CP Ibrahim Adamu Bakori.
Shugabar Kungiyar mata lauyoyin Barista Nafisa Abba Isma’il, ita ce ta jagoranci gudanar da zanga-zangar don nuna rashin amincewarsu da kiran da gwamnan Kanon ya yi.
Yayin gudanar zanga-zangar an sami fitowar mata da kungoyoyi da dama inda aka rika daddaga kwalaye dauke da rubuce-rubuce, tare da kira ga babban sufeton yan sandan ,Kayode Egbetokun, ya bar kwamishinan a kano a bisa hujjar cewa ya na iya bakin kokarin ganin ya tabbatar da tsaro da kare rayukan alúmma da dukiyoyinsu a fadin jahar kano.
- Yan Sandan Kano Sun Kama Wadanda Ake Zargi Da aikata Laifuka Mabambanta
- Siyasa Da Tsaro: Gwamnan Kano Ya Tura Neman A Sauya Kwamishinan Yan Sandan Jihar.
Daga bisani an gudanar da addu’o’i a wurin taron zanga-zangar da kuma kira da babbar murya ga Sufeton ‘Yan sanda na kasa da ya ci gaba da ba da hadin kai ga kwamishinan yan sanda CP Ibrahim Adamu Bakori.
Tun dai a yayin bikin cikar Nigeria shekara 65 da samun ‘Yancin kai a ranar 1 ga watan Oktoba 2025 , gwamnan Jahar Kano Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga Shugaban kasa da ya sauya kwamishinan yan sandan, bisa hujjar an janye jami’an yan sanda kuma kwamishinan yaki halattar bikin faretin da aka shirya yi a filin wasa na Abacha kano.
Koda ya ke zuwa wannan lokaci wamishinan ‘Yan sanda jahar kano CP Ibrahim Adamu Bakori bai ce komai ba kan zargin da gwamnan Kanon ya yi.