Rundunar yan sandan jahar Kano , ta bayyana cewa ta cafke mutane 269, wadanda ake zargi da fakewa da zanga-zangar matsin rayuwa, domin diban ganima, tare da tayar da hankulan jama’a da sace-sace da kuma barnata dukiyar gwamnati da ta al’umma.
Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano , SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
Idongari.ng, ta ruwato, yan sandan sun kwato jarkokin man gyada, kayan abinci da sauran kayayyaki ma su yawa daga hannun mutanen wadanda suka hada da maza da mata.
Kwamishinan yan sandan jahar CP Salman Dogo Garba, ya ce nauyin da ya rata ya a wuyansu shi ne, su kare rayukan al’umma da kuma dukiyoyinsu, kuma duk wanda ya yi yunkurin haifar da rudani ko satar kayan gwamnati da kuma yada labaran karya ba za su saurara masa ba domin zai fuskanci hukunci.
Sanarwa ta yi kira al’umma da su mutunta dokar hana fita da gwamnatin jahar Kano ta sanya tsawon awanni 24.
A karshe SP Abdullahi Haruna Kiyawa dukkan wanda ake zargi suna sashin gudanar da binciken laifuka kuma da zarar an kammala gudanar da bincike za a gurfanar da su a gaban kotu don su fuskanci hukunci.