Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya gana da ƙananan yaran da aka kama yayin zanga-zangar #EndBadGovernance a Fadar Shugaban Ƙasa, da ke Abuja.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne, ya bayar da umarnin sakin yaran tare miƙa su ga iyayensu.
An shirya ganawarsu da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wanda zai miƙa su ga gwamnonin jihohinsu don tsara yadda za su bar Abuja.
Tun da farko, an gurfanar da yaran masu zanga-zangar a kotu bayan rundunar ’yan sandan Najeriya ta kama su.
Amma daga bisani Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sallame su.
- Kano: Wata Kotu Ta Bayar Da Umarnin A Bincika Kwakwalwar Wata Mata Bayan Ta Furta Wasu Kalamai
- Hukumar CISA Tace Ba Za A Iya Yin Katsalanda A Zaben Shugaban Kasar Amurika Ba
Mai shari’a Obiora Egwatu, na babbar kotun ya soke tuhumar da ake musu, bayan da Antoni-Janar na Tarayya, Lateef Fagbemi, ya nemi a soke shari’ar.
Gwamnonin Kaduna da Kano suna Fadar Shugaban Ƙasa domin halartar taron, tare da ministocin ma’aikatu daban-daban kamar Ilimi, Harkokin Jin-Ƙai da Rage Talauci, Muhalli.
Sauran sun haɗa da manyan jami’an gwamnati daga ma’aikatu daban-daban.