Zanga-zanga: Yan Sanda A Jigawa Sun Cafke Mutane 55 Bisa zargin Barnata Dukiya Da Sata

Spread the love

Rundunar Yan sandan jahar Jigawa ta tabbatar da cafke mutane 55, da ake zargi barna kayan jama’a da na gwamnati ta hnayar kunna wuta da kuma sata.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jahar Jigawa DSP Lawan Shiisu Lawan Adamu, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aike wa da manema labarai a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce wadanda ake zargin sun shiga sakatariyar karamar hukumar Hadejia tare da kunawa ababen hawa 6 wuta, sannan sun lalata Jarda Store, Jasco, tare da diban takin zamani da kuma kayan abinci a karamar hukumar Gumel.

DSP Shiisu Lawan ya kara da cewa , matasan sun kunna wuta a gidan dan majalissar dokokin tarayya Hon. Nazifi Sani , tare da barnata ofishin NITDA , bayan sun cinna wuta a sakariyar jam’iyar APC dake jahar.

Haka zalika sun yi yunkurin cinna wuta a gidan dan majalissar dattawa Sanata Babangida Aliyu, a karamar hukumar Kazaure.

Rundunar ta samu nasarar kwato Babura 35, adaidaita sahu 3, Kekuna 12,  buhunan takin zamani 111, kujeru 9 da kuma katon 40 na ragar gidan sauro.

Yanzu haka dai an sanya dokar hana fita tsawon a wanni 24.

A karshe rundunar ta ce ta na ci gaba da gudnaar da bincike kan lamarin.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *