Zuzzurfan rarrabuwar kan siyasar Isra’ila ta sake dawowa sabuwa fil a kan idon jama’a.
Tsawon wani ɗan lokaci, an jingine su wuri ɗaya, yayin da kaɗuwa da rajin haɗin kan ƙasa suka biyo bayan hare-haren ranar 7 ga watan Oktoba na mayakan Hamas – sai dai wata shida bayan nan, dubun dubatar masu zanga-zanga sun sake fantsama a kan titunan Isra’ila.
Yaƙin da ƙasar ke yi, ya sake yi musu ƙaimi a ƙudurinsu na kawo ƙarshen mulkin Firaminista Benjamin Netanyahu, mafi dogon zamani.
A Ƙudus, ‘yan sanda sun yi amfani da ruwan ɗoyi wajen fesa wa masu zanaga-zangar da rufe babban titin arewa zuwa kudu.
- An Sace Ɗalibai 3 A Jami’ar Kalaba
- Yadda gwamnonin jihohi 13 suka ci bashin kusan naira biliyan 250 a wata shida
Wasu a cikinsu na ta rera taken Netanyahu ya sauka daga mulki sannan a gudanar da zaɓen wuri, yayin da wasu ke nanata kiran a gaggauta sako ‘yan Isra’ila kimanin 130 da ake garkuwa da su a Gaza. Ana dai jin cewa akwai wani adadi daga cikinsu da ya rasu.
Babbar fargabar masu zanga-zangar ko danginsu da abokan arziƙi, ita ce ƙarin waɗanda ake garkuwar da su, za su yi ta mutu idan aka ci gaba da gwabza yaƙin ba tare da an bi matakin sulhuntawa ba.