A karon farko a arewacin Najeriya an samu musayar yawu tsakanin malaman addini da matasa a kafafen sada zumunta, inda har ta kai ga zage-zage da barazana.
Wannan dai ya biyo bayan yekuwar yin zanga-zanga da wasu matasan arewacin ƙasar suke yi a soshiyal midiya sakamakon abin da suka kira “matsananciyar rayuwa” da jama’ar yankin ke ciki, inda wasu malamai kuma suka fara jan hankalin cewa zanga-zangar “haramun” ce a addinin Musulunci.
Al’amarin ya ƙara rincaɓewa a makon da ya gabata bayan wani matashi ya fito yana kira ga ƴan’uwansa matasa da su “kifar” da duk malamin da ya hau mumbari ya ce zanga-zanga haram ce.
An kuma samu wasu ɗaiɗaikun matasa da suka rinƙa fitowa a cikin bidiyo daban-daban suna gargaɗi ga malamai, inda suke cewa malaman ba sa tausaya musu dangane da halin da suke ciki.
Har wayau, an samu yanayin da wasu suka ƙirƙiro rasitai na boge da ke ɗauke da sunayen wadansu malamai da kuma adadin kudin da suka ce an ba su.
Martanin malamai
Tun bayan fitar bidiyon kiran a “kifar” da malamin da ke haramta zanga-zangar da kuma bidiyon yadda za a aiwatar da hakan, malamai da dama na arewacin Najeriya suka fara mayar da martani.
An ga bidiyon malamai da dama da suka yi gargaɗin cewa za su ɗauki matakin ramuwa ga duk matashin da ya nemi gwada “kifar” da su daga mumbari, inda wani malami ya ce “na yi kama da mutumin da za a kifar? Kai ka dube ni ka gani. Wallahi da an yi kife-kife.”
Wani yankin bidiyo wanda da alama an ciro shi ne daga wata huɗuba da sheikh Sanusi Khalil, malamin addinin Musulunci ya yi ranar Juma’ar da ta gabata, ya nuna yadda malamin ke gargaɗi ga duk mutumin da ke shirin “kifar” da shi.
- An samu raguwar kashe-kashe da garkuwa da mutane a Najeriya – Rahoto
- Cikin Hotuna: Yadda Matasa 136 Suka Baje-Kolin Fikirarsu A Kano
Malamai ne suka koya wa mabiya zage-zage – Ibrahim Khalil
Fitaccen malamin addinin nan na Najeriya kuma tsohon ɗan takarar kujerar gwamna a Kano, Sheikh Ibrahim Khalil ya bayyana wasu abubuwa guda uku da ya ce su ne dalilan zaman tankiyar a tsakanin ɓangarorin biyu:
- Ƙoƙarin rusa darajar malamai: Akwai wasu mutane a ɓoye da ke ƙoƙarin rusa darajar malamai kamar yadda aka karya darajar sarauta. To wannan ma ya taimaka wurin wannan rikicin.
- Matasan Malamai da ke zagin malamai ƴan uwansu: Akwai matasan malamai da ke zagi ko kuma faɗa wa malamai ƴan uwansu magana maras daɗi wanda kuma hakan na koyawa mutane cewa su ma su yi irin wannan cin-mutumci ga wani malami.
- Malaman fada: Akwai kuma malaman fada waɗanda suka kanainaye shugabanni har ta kai ga jama’a suna tunanin ba su da banbanci da shugabannin da suke tunanin suna “zaluntar” su.
Shi ma Dakta Elharoon Muhammad tsohon malami a tsangayar nazarin siyasa da diflomasiyya a kwalejin fasaha ta gwamnatin tarayya da ke Kaduna kuma mai sharhi kan al’amura, ya ce “duka wannan matsala za ka iya kasa ta gida uku ko huɗu.”
“Misali yanzu Idanun jama’a sun buɗe ma’ana jama’a na karatu saɓanin a baya da malami zai fadi abin da ya ga dama ba tare da samun inkari ba daga jama’a.
Sannan hakan na nufin za a iya yi wa malamai turjiya ka kenan hakan ya nuna akwai matsala ko dai tsarkin zuciyar malaman ba ta da tsarki ko kuma akwai abin da suka sa a gaba wanda bai yi wa jama’a daɗi ba.
Haka kuma wannan al’amari yana ƙara fito da cewa ba zai yiwu masu mulki su rinƙa yin abin da suka ga dama ba kuma malamai su hana al’umma magana.” In ji dakta Elharoon Muhammad.
Mece ce mafita?
Sheikh Ibrahim Khalil da dakta Elharoon Muhammad duk sun amince cewar mafita ga wannan zaman tankiya da aka fara tsakanin malamai da matasa ka iya zame wa yankin arewacin Najeriya babban ƙalubale.
Sai malaman biyu sun ce har yanzu ba a makara ba, inda suka kawo wasu hanyoyin da ya kamata a bi domin magance matsalar tun kafin ta gagari Kundila.
- Malamai su ji tsoron Allah.
- Malamai su daina sakin baki ga ƴan uwansu malamai.
- Malamai su daina zama masu magana da yawun gwamnati musamman idan ta ‘kauce hanya’.
- Matasa su ɗauki malamai a madubin rayuwa domin idan aka raina malamai to rayuwar al’umma za ta yi muni domin malamai ne jagororin al’umma.
Wannan al’amari dai da ke faruwa a karon farko na faɗi-in-faɗa tsakanin malamai da matasan arewacin Najeriya ya kamata ya zama wani darasi ga dukkan ɓangarorin biyu na arewacin Najeriya domin samun kyakkyawar makoma tun da dukkan ɓangarorin biyu na buƙatar juna.
BBCH