Zanga-zangar tsadar rayuwa: An kashe aƙalla mutum 24, an kama 1,200 – Amnesty International

Spread the love
endbada

Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta ce ƴansanda sun yi amfani da ƙarfi a kan waɗanda suka yi zanga-zangar a tsakanin ranakun 1 zuwa 10 ga watan Agusta.

Rahoton ƙungiyar ya ƙara da cewa an kashe aƙalla mutum 24 a jihohin Borno da Kaduna da Kano da Katsina da Jigawa da Neja, kamar yadda rahoton ƙungiyar ya bayyana.

“Ƴan Najeriya sun fuskanci rashin amfani da doka, inda jami’an tsaro suka yi amfani harsasai a kan masu zanga-zangar tsadar rayuwa. Daga cikin waɗanda aka kashe matasa guda 20, da wani dattijo da ƙananan yara guda biyu,” in ji shi sanarwar, wadda Isa Sanusi, daraktan ofishin a Najeriya ya sa wa hannu.

Rahoton ya ƙara da cewa waɗanda aka kashe za su iya haura 24 “saboda gwamnatin ta ɓoye ainihin abin da ya faru.

A cewar rahoton: “Dole ne gwamnatin Najeriya ta tuhumi ƴansanda da jami’an tsaro bisa amfani da ƙarfi a kan masu zanga-zangar lumana. Akwai mamaki yadda ƴansanda suke cewa ba su aikata laifin komai ba, duk da dalilan da suka bayyana.

“Dole shugaban ƙasa Bola Tinubu da gwamnatinsa su gabatar da bincike akan zargin cin zarafin masu zanga-zangar, sannan a tabbatar a hukunta waɗanda aka kama da laifi.

“An kashe mutum 12 a Rijiyar Lemo da Ƙofar Nasarawa. A Jigawa an kashe mutum 3 a Hadejia, sannan aka kashe mutum 1 a Ƙofar Sauri a Katsina. A Kaduna wani soja ya kashe wani ƙaramin yaro a Zaria, sannan ƴansanda sun kashe mutum a cikin Kaduna. A Maiduguri an kashe mutum 3 a gidan man A.A Kime da ke mahaɗar Bolori. A Neja, an kashe mutum uku a titin Abuja-Kaduna.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *