Rundunar ‘yansandan birnin tarayya, Abuja ta ce za ta jibge isassun ‘yansanda a faɗin birnin, gabanin zanga-zangar tsadar rayuwa da ake shirin gudanarwa a faɗin ƙasar.
“Za mu ɗauki matakin ne da nufin tabbatar da tsaron al’umma da masu zanga-zangar da kuma magance shigar ɓata-gari cikin zanga-zangar domin aikata ɓarna”, kamar yadda kakakin rundunar ‘yansandan birnin, SP Josephine Adeh ta bayyana cikin sanarwa.
“Haka kuma za mu girke kayan aiki ciki har na’urorin gano ababen fashewa, da ƙwararrun ma’aikata a fannoni daban-daban a sassan birnin”.
“Sannan kuma jami’anmu za su dirar wa duk wasu mutane ko wuraren da ba ta yarda da su ba, kamar gine-ginen da ba a kammala ba da sauran wurare, haka kuma jami’anmu za su riƙa binciken mutane da ababen hawa ta hanyar aiki da sauran jami’an tsaro”, in ji sanarwar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa rundunar ‘yansandan birnin ta ce ba za ta lamunci tayar da rikici ko saɓa wa doka don kauce wa tashin hankalin da ka iya janyo asrar rayuka da dukiya a lokacin zanga-zangar.