Babbar kotun jahar Kano, mai lamba 17 , karkashin jagoranci mai Shari’a Amina Adamu , ta sanya karfe 2:30pm na Rana don bayyana matsayarta kan batun gurfanar da tsohon gwamnan jahar Dr. Abdullahi Umar Ganduje da mai dankinsa Farfesa Hafsat Ganduje da kuma mutane shida.
Ya yin zaman kotun na Ranar Alhamis, lauyoyin gwamnatin jahar, sun bayyana wa kotun cewa an sadar da sammacin ga wadanda ake karar ta hanyar kafafen yada labarai kamar yadda kotun bayar da umarni tun a baya.
Sai dai wadanda ake karar ba Su halacci zaman kotun ba, a dan haka ne lauyoyin gwamnatin jahar Kano, syka roki kotun ta bayar da umarnin kamo su ko kuma kotun ta ci gaba da sauraren shari’ar duk da ba Su samu damar halattar zaman ba.
- EndSars: Kotun Ecowas Ta Samu Gwamnatin Nigeria Da Laifin Ta Ke Hakkin Dan Adam
- Ƙungiyoyin ƙwadago na duba yiwuwar amsa gayyatar Tinubu
A bangaren Wanda ake karar na shida, Barista Nuraini Jimoh, ya soki rokon lauyoyin gwamnatin jahar Kano, inda ya ce kotun ta Dakata sakamakon daukaka karar da suka Yi, kuma kotun bata da hurimin sauraren shari’ar.
Barista Jimoh, ya kara da cewa kunshin tuhume-tuhumen suna dauke da kura-kurai.
Gwamnatin jahar Kano ce ta Yi karar tsohon gwamnan jahar Abdullahi Umar Ganduje da wa Su mutane shida bisa zargin almundahanar kudi fiye da naira biliyan 4, da ake zargin an siyar da wasu filaye tare da raba kudaden a tsakaninsu.
Kotun za ta bayyana matsayar ta da misalin karfe 2:30pm kan shari’ar.
A karshe kotun ta Hana lauyoyi yin magana da manema labarai.