Rundunar yan sandan jihar Kano, ta gayyaci wasu mutane 30 don amsa tambayoyi a ofisoshin baturen yan sandan kananan hukumominsu kan wasu zarge-zarge da ake yi musu.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa , ne ya bayyana hakan a wajen taron masu ruwa da tsaki kantsaro da aka shiryawa , al’ummar kananan hukumomin Shanono, Bagwai, Gwarzo , Tsanyawa da kuma Bichi, don tattaunawa da su sakamakon barazanar masu garkuwa da mutane a yankin.
A makonnin da suka gabata an samu rahotannin yadda yadda masu satar mutane suke shiga wasu garuruwa musamman a karamar hukumar Shanono, inda suke sace mutane duk da cewa hukumomin tsaro na iya bakin kokarinsu don magance matsalar baki daya.
kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu ne ya jagoranci tawagar dakarun yan sanda, zuwa kananan hukumomin, har suka yi rangadin bin dukan iyakokin kananan hukumomin da jihar Katsina don tantancewa da kuma daukar matakan gaggawa kan tsaro.
- Shugabar Matan PDP Shiyar Arewa Maso Yamma Ta Bukaci Gwamnan Kano Abba K. Yusuf Ya Dawo Jamâiyar.
- Jubilations As Kano State Police Command Arrests Suspected Kidnapper, Rescue A 75 Year Old Victim
sunayen mutanen da rundunar yan sandan ta gayyata sun hada , Inusa Abdullahi wanda akafi sani da Inunriga Majingini, Bello Lawan Tuli Majingini, Mai unguwar Kanawa Bagwai, Ado Alhaji Kwarijo gidan Jobawa, Kwallo a Raga dake Romo, Abba Bosho Bagwai, Chabe Gaye Bagwai, Abdullahi Zangonre baure, Sama’ila Fulani Baure, Kabiru Mai Nama Alajawa, Yusha’u Kadiri Alajawa, Ya’u Kadamu, Isiyaku Danmakura dake Kuraku Faruruwa sai kuma Rufa’i Gwarzo.
Sauran sunayen sune, Sabi’u Gwarzo, Nasiru Danladi Gwarzo, Habila Bagwai, Lado Wartu, Salisu Bagwai, Lado Gezawa, Mamman Kabo, Habu Gajere Dunbulun, Siniya Dunbulun, Duwa Dunbulun, Abdul Garo , Sarkin fawa Zaroji Tsanyawa da kuma Mai Chibi Zaroji.
SP Abdullahi Kiyawa ya ce dukkan mutanen da aka ambaci sunayensu za a zauna da su ne kan wasu bayanan da aka samu akansu don tantancewa , kuma duk wanda aka samu da hannu wajen aikata laifuka za a sake jin sunansa cikin wadanda ake zargin.
Al’ummar yankunan da lamarin ya shafa sun koka tare da cewa akwai wadanda suke zaune a cikinsu kuma su suke zargi da taimakawa yan ta’addar da bayanan sirri.
Taron an gudanar dashi a garin Faruruwa dake karamar hukumar Shanono.
Kananan hukumomin da lamarin ya shafa suna arewacin Kano kan iyaka da jihar Katsina dake fama da matsalar yan bindiga da garkuwa da mutane don neman kudin fansa.