Babbar kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta, a unguwar Rijiyar Zaki Kano, karkashin jagorancin Mai Shari’a Halhalatul Kuza’i Zakariyya , ta dage ci gaban Shari’ar da Ake Yi wa Matashin nan , Mai suna Shafi’u Abubakar, bisa Zargin sa da Cinnawa masallata wuta a Garin Gadan dake karamar hukumar Gezawa ta jahar.
Kotun ta sanya wannan rana domin fadar ra’ayin ta kan shaidun da aka gabatar mata, Inda kotun ta dage zaman Zuwa ranar 4 ga watan Disamba 2024 don yin nazari da kuma fadin ra’ayin ta.
Ana zargin Shafi’u Abubakar, da kunnawa masallata wuta, ta hanyar zuba Fetur , har mutane 23 suka rasa rayukan su.
Sai dai Wanda Ake tuhumar ya bayyana cewa, a shirye yake ya karbi duk hukuncin da zai biyo baya, kuma baya fatan ci gaba da zama a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya, yafi so a kashe shi.