Kakakin rundunar ƴansandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi, ya ce zagin mutane a kafofin sadarwa laifi a ƙarƙashin dokokin Najeriya, wanda kuma duk wanda ya aikata zai iya fuskantar hukunci.
Adejobi ne ya wallafa shakan a shafinsa na X, inda ya ce: “zagin mutane a kafofin sadarwa ba furta albarkacin baki ba ne.
“Cin zarafi ta kafafen sadarwa na, wadda kuma daban yake da ɓata suna. Kuma laifi ne babba, wanda mai aikatawa zai iya fuskantar hukunci. A bi a hankali.”