Zargin N110.4bn: Kotu ta bada belin Yahaya Bello kan N500m

Spread the love

 

Wata babbar kotu a Abuja ta bayar da belin tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello a kan kuɗi Naira miliyan 500 bisa zargin karkatar da kuɗaɗen gwamnati.

Mai shari’a Maryanne Aninih ce ta bada umarnin a ranar Alhamis ta kuma umurci Bello da ya gabatar da waɗanda za su tsaya masa guda uku a daidai wannan adadin kuɗin.

Alƙalin ta ce dole ne waɗanda za su tsaya masa su kasance fitattun ’yan Najeriya da ke da kadarori a ɗaya daga cikin unguwannin Maitama da Jabi da Utako da  Apo da Guzape da Garki da Asokoro.

Alkalin ta kuma buƙaci Yahaya Bello da ya ajiye fasfo ɗinsa da sauran takardun tafiye-tafiye a wurin magatakardar kotun

Ta kuma bayar da umarnin cewa dole ne ya ci gaba da zama a gidan gyaran yarin Kuje har sai an cika sharuɗɗan belin.

Mai shari’a Maryann Anenih, a ranar 10 ga watan Disamba, ta ƙi amincewa da buƙatar belin tsohon gwamnan, tana mai cewa an shigar buƙatar ne da wuri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *