Rundunar Yan Sandan Nijeriya, ta gayyaci shugaban kungiyar kwadago ta kasa NLC, Joe Ajaero, domin amsa wasu tambayoyi da suka shafi zargin alaka da kudaden ta’addaci, cin amanar kasa da kuma aikata laifukan yanar gizo.
Wasikar gayyatar mai dauke da sa hannun mataimakin kwamishinan yan Sandan sashin IRT, ACP Adamu S. Mu’azu.
Rundunar Yan Sandan Nijeriya ta bukaci Joe Ajaero, ya mutunta gayyatar a ranar Talata 20/8/2024 da misalin karfe 10:00am na safe, idan kuma yaki Amsa gayyatar za a iya Sanya wa a kama shi.