Zargin Zamba: Yan sandan Kano sun kama Darakta da mutane 2 bisa zargin yin gwanjon kaya ba bisa ka’ida ba

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Kano ta cafke Darakta ma’aikatan ruwa na jahar, Abubakar Gambo, mai shekaru 49 , tare da wasu mutane biyu, bisa zarginsu da hada kai da yin gwanjon wasu Famfunan kayan Nomin Rani.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna, ya ce mutanen da ake zargi, sun rubuta wata takadda ba tare izinin kwamishinan ma’aikatar ruwan ba, inda suka yi gwanjon fanfunan da kuma wani Tankin ruwa da aka samar domin Noman rani wadanda ke da mutukar muhimmanci ga rayuwar al’umma.

Sauran wadanda aka cafke din sun hada da Nuhu Mansur Tsohon Manaja shirin Noman Rani na Karafe a karamar hukumar Tudun Wada da kuma mataimakin sakataren gudanarwa Baba Yahya, wadanda aka kama su a karamar hukumar Tudun Wada Kano.
Binciken yan sanda na farko- farko , wadanda ake zargin sun amsa laifinsu tare da cewa sun siyar da kayan akan kudi naira dubu dari biyar (N500,000:00).

SP Abdullahi Kiyawa ya kara da cewa, an samu nasarar dawo da kayan da kuma tsabar kudi naira dubu dari biyar (N500,000:00) a wajen Abubakar Gambo , kuma da zarar an kammala gudanar da bincike za a gurfanar da shi a gaban kotu dan ya fuskanci hukunci.
Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel , ya bukaci al’umma da su za mo, ma su lurara akoda yaushe dan tallafawa yan sanda wajen kama batagari da ke satar kayan gwamnati.

A karshe kwamishinan ya godewa jama’ar jahar bisa goyon bayan da suke ba su a koda yaushe, sai dai ya bukace su a duk lokacin da suka ga wani abu da ba su amince da shi su yi gaggawar sanarwa a ofishin yan sanda mafi kusa dan daukar matakin da ya dace.

kota Nambobin waya 08032419754, 08123821575, 09029292926,
ko ta shafukan sada zumunta
Facebook: Kano State Police Command
Twitter: Kano State Police Command (@KanoPoliceNG)
Instagram: Kano State Police Command
Tiktok: Kano State Police Command.
or log in to the NPF Rescue Me Application available in the Play Store.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *