Zone 1: An Tallafa Wa Iyalan Yan Sandan Da Suka Rasa Rayukansu Da Kayan Abinci A Kano.

Spread the love

Mataimakin Babban sufeton Yan sandan Nigeria, mai kula da Shiya ta daya ( Zone 1 Kano) AIG Umar Muhammed Sanda, ya yi Kira ga al’umma da su ci gaba da tallafawa jami’an Yan sanda, musamman iyalan wadanda suka rayasa rayukansu.

AIG Umar Sanda, ya bayyana hakan a yayin rabon kayan abinci, da aka tallafawa, iyalan wadanda Suka rasa rayukansu , Wanda aka gudanar a rundunar Yan sandan Nigeria Shiya ta daya a jahar Kano.

Ya Kara da cewa, a irin wannan lokacin ne suke tuna wa da Yan uwansu da Suka rasa rayukansu, wajen tallafa wa iyalansu da kayan abinci, Wanda Suka yi karo-karo a junansu da kuma Wanda al’ummar gari Suka taimaka.

Umar Sanda , ya ce za su ci gaba da yin wannan Abu har tsawon rayuwarsu, Wanda hakan zai nuna cewa ana tare da iyalan wadanda suka rasa.

” kamar yadda muke fada shi dan sanda mutanen gari yake yi wa aiki, kuma ya sadukar da kansa wajen hidimta mu su, Wanda ya zama wajibi al’umma su taimaka mu su a duk lokacin da hakan ya taso”.

Babban Limamin masallacin juma’a na Rundunar Yan sandan Nigeria Shiya ta daya, CSP Muhammed Kabir Abubakar, ya ce duk shekara, a irin wannan lokaci na azumin ramadana sukan taimaka wa iyalan jami’an Yan sandan da Suka rasu, domin rage mu su radadin rayuwa.

CSP Muhammed Kabir, ya Kara da cewa a wannan shekarar sun tallafawa mutane 38, kowannensu shinkafa Kwana biyar , Taliya guda biyar da kuma kudin mota.

Tallafin kayan Abincin an tattara shi ne, karkashin babban limamin masallacin Rundnar Yan sandan Nigeria shiya ta daya CSP Muhammed Kabir Abubakar ,da kuma babban limamin rudunar yan sandan Jahar Kano CSP Dr. Abdulkadir Haruna.

Wadanda suka amfana da tallafin kayan abincin sun bayyana Farin cikinsu tare da yin godiya Allah ya saka da alkairi sakamakon sanya mu su farin ciki da ake yi akoda yaushe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *