Zulum ya ɗage dokar taƙaita zirga-zirga a Borno

Spread the love

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya ɗage dokar taƙaita zirga-zirga da aka sanya a jihar, bayan fashewar bom a Kawori ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 16 tare da jikkata wasu.

Yayin da yake jawabi da aka yaɗa a kafofin yaɗa labaran jihar, Gwamna Zulum ya jajanta wa iyalan waɗanda suka mutu a harin na Kawori.

”Ina miƙa saƙon ta’aziyyar ga iyalan waɗanda harin ya shafa da kuma duka mutanen Borno, ina kuma jajanta wa waɗanda suka jikkata, waɗanda a yanzu haka ke asibiti suke kuma samun kulawar likitoci”.

Gwamnan ya kuma ce tun da farko an sanya dokar ne domin hana mayaƙan Boko Haram amfani da damar wajen haifar da tashin hankali a jihar.

Ya ƙara da cewa ɓata-gari ne suka yi shigar burta domin shiga cikin masu zanga-zangar lumana, inda suka yi yunƙurin kawo hargitsi, sai dai a cewarsa jami’an tsaro sun samu nasarar kwantar da hankula.

Yayin da yake bayyana janye dokar taƙaita zirga-zirgar, Gwamna Zulum ya ce mutane su fita harkokinsu, amma jami’an tsaro za su ci gaba da sanya idanu, domin magance duk wani abu da suka ga zai kawo tashin hankali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *