Ƙudirin ƙirƙiro ƴan sandan jihohi ya tsalake karatu na biyu a zauren majalisa

Spread the love

Ƙudirin ƙirƙiro da ƴansandan jihohi a Najeriya ya tsalake karatu na biyu a zauren majalisar wakilai.

Ƙudirin wanda ƴan majalisar 13 suka ɗauki gabatar, ya samu goyon bayan mafi rinjayen ƴan majalisar waɗanda suka yi imanin cewa gwamnonin jihohi ya kamata su mayar da hankalinsu ga halin da ake ciki na rashin tsaro a fadin kasar.

A makon da ya gabata, Shugaba Bola Tinubu da gwamnonin jihohi 36 suka tattauna kan batun samar da ƴansandan jihohi don magance matsalolin tsaro da ke barazana ga ƙasar, waɗanda suka haɗa da satar mutane da fashi da makami da suka zama tamkar ruwan dare.

Ƙirƙirar ƴansandan jihohi dai ta kasance batun da ya daɗe ana muhawara a kai a ƙasar.

Gamayyar hukumomin tsaro a Kano sun tattauna da shugabancin jam’iyun siyasa gabanin zaben cike gibi da za a sake yi a Kunchi/Tsanyawa.

Wata mata ta haihu a tashar mota a Najeriya

Gwamnonin da aka zaɓa a karkashin jam’iyyar PDP a baya-bayan nan sun sake jaddada muhimmanci ƙirƙirar ƴansandan jihohin, a matsayin mafita ga taɓarɓarewar tsaro a ƙasar.

Har ila yau, kungiyoyin siyasa da na al’umma irin su Afenifere da Ohanaeze Ndigbo da Middle Belt Forum, sun sha yin kira da a kafa ƴansandan jihohi domin magance mummunan ƙalubalen tsaro da ke addabar al’ummar Najeriya.

Tuni dai jihohi a shiyyar Kudu-maso-Yamma sun kafa kungiyar Amotekun yayin da takwarorinsu na yankin Kudu maso Gabas suma suka ƙirƙiri jami’an tsaro da suke kira Ebube Agu. Haka kuma Benue ta kafa ‘The Benue guards’ kuma sun fara aiki da dai sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *