Ƙungiyoyi sun allawadai da kamun matashi da gwamnatin jihar Sokoto ta yi

Spread the love

Gamayyar Kungiyoyin Kare Haƙƙin ɗan Adam da na Matasa a Jihar Sokoto sun koka da kama wani matashi a jihar.

Ƙungiyoyin sun bayyana koken ne a cikin wata takarda da suka fitar, inda suka yi Allahwadai da tsare matashin mai Shafiu Umar Tureta, mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga tsohon gwamnanar jihar, Sanata Aminu Waziri Tambuwal da ake zargin gwamnatin Jihar ta sa aka yi da kuma gurfanar da shi gaban kotu.

Ƙungiyoyin sun ce tsare Tureta cin zarafi ne ga ƴancin ɗan adam.

A cewar takardar koken, ƴan sanda sun kama Tureta bisa umarnin gwamnatin jihar bayan ya yaɗa wasu bidiyoyi a shafin sada zumunta na Facebook wanda ke nuna Gwamnan Jihar Aliyu na ƙoƙarin yin magana da Ingilishi da kuma wani wanda ya nuna shi yana liƙa dalar Amurka a wajen bikin zagayowar ranar haihuwar uwargidan gwamnan.

Lamarin da ya janyo suka daga ɓangarori da dama bisa la’akari da irin halin matsi da ake ciki a Najeriya.

Ƙungiyoyin sun bayyana cewa yayin da matar gwamnan da sauran waɗanda suke liƙin a cikin bidiyon ba su fuskanci wani hukunci na shari’a ba, bai kamata a hukunta Tureta ba kan wallafa bidiyon.

Takardar ta jaddada cewa kamun Tureta ya saɓa wa ‘yancin faɗin albarkacin baki da tsarin mulki ya tanadar.

Ƙungiyoyin sun kuma yi kira ga Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta shiga tsakani, inda ta buƙace ta da ta shawarci gwamnatin Jihar Sokoto da ɓangaren shari’a da su kaucewa wa ayyukan da za a iya ɗauka a matsayin cin zarafi na ‘yan kasa.

Sun kuma buƙaci a gaggauta sakin Tureta ba tare da wani sharaɗi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *