Ƙungiyoyin ƙwadago na duba yiwuwar amsa gayyatar Tinubu

Spread the love

Shugabannin haɗakar ƙungiyoyin kwadago a Najeriya na duba yiyuwar amsa gayyatar da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya yi musu zuwa fadarsa don tattauna batun mafi ƙanƙantar albashi.

Tun da farko shugaban ƙasar, Bola Tinubu ne ya aike wa shugabannin ƙungiyoyin wasiƙa buƙatar tattaunawa da su a fadarsa a yau Alhamis kan mafi ƙanƙantar albashin ma’aikata da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a ƙasar.

To sai dai wata majiya daga ƙungiyar NLC ta shaida wa BBC cewa ƙungiyoyin ƙwadagon sun samu gayyatar da shugaban ƙasar ya yi musu, kuma shugabanninsu za su zauna domin yin nazarin wasiƙar gayyatar da shugaban ƙasar ya yi musu.

Majiyar NLCn ta ce idan shugabannin nata suka zauna za su tattauna tare da yin nazarin wasiƙar shugaban ƙasar, domin duba yiyuwar amsa gayyatar ko akasin hakan.

Ƙungiyoyin ƙwadagon da gwamnatin Najeriya dai sun jima suna kai ruwa rana kan mafi ƙanƙantar albashin ma’aikata a ƙasar.

Ita dai gwamnatin Najeriya ta yi wa NLC tayin biyan naira 62,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashin, yayin da ita kuma NLC ke buƙatar gwamnatin ta biya naira 250,000.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *