Ƴan majalisar dokokin Rivers 27 sun fice daga PDP

Spread the love

Ƴan majalisar dokokin jihar Rivers 27 cikin su 32 sun fice daga Jam’iyyar PDP mai mulki a jihar zuwa APC.

Ƴan majalisar dokokin sun sanar da matsayarsu ne a wani taro da suka yi yau Litinin.

An kuma ga wani bidiyo da yake yawo a shafukan sada zumunta inda yan majalisar ke ɗauke da tutar APC.

Sun ce babban dalilin da ya sa suka sauya sheƙa shi ne rarrabuwar kan da aka samu a jam’iyyar PDP.

Lamarin dai ya ƙara zafafa rikici tsakanin gwamnan jihar, Siminalayi Fubara da ƴan majalisar dokokin da ke yi wa tsohon gwamna Nyeson Wike mubaya’a

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *