Ƴan Najeriya na jiran sakamakon bincike game da sojan ruwa Abbas

Spread the love

Ana ci gaba da zazzafar mahawara shafukan sada zumunta a Najeriya game da zargin cin zarafi da kuma azabtar da wani sojan ruwa bayan da matarsa ta bayyana cewa an ɗaure shi tsawon shekara shida cikin mummunar yanayi har ya samu taɓin hankali.

A cikin wani faifan bidiyo matar sojan ruwan mai suna Abbas Haruna ta bayyana cewa an gana masa uƙubar da ta wuce misali.

Matar mai suna Hussaina ta bayyana ne a wani shiri na gidan talabijin na ‘Brekete Family’, inda a ciki ta bayyana wasu zarge-zargen cewa ba a yi wa mijinta da ma su iyalansa ɗin adalci ba.

Hussaina, wadda ake kira Maman Shahid, ta bayyana cewa mijin nata ya samu saɓani ne da wani babban hafsan soja, inda tun a lokacin aka kama shi, aka tsare, kuma a cewarta kusan shekara shida ke nan yana tsare.

Bidiyon na Hussaina ya karaɗe shafukan sada zumunta, inda aka riƙa yaɗa shi, wasu na zagi, wasu na Allah wadai, wasu kuma suna cewa a dai yi bincike.

Babban abin da ya ja hankalin mutane shi ne yadda Hussaina ta bayyana yadda ta sha faɗi-tashi da tafiye-tafiye tsakanin Kaduna da Taraba da Abuja da Gombe duk a kan mijin.

Shalkwatar tsaro da majalisa za su gudanar da bincike

Shalkwatar tsaron Najeriya ta ce ta ga bidiyon wanda a ciki aka yi zargin tsare wani sojan ruwa mai suna Seaman Abbas Haruna tsawon shekara shida kuma tana bincike a kai.

Shalkwatar a wata sanarwa da kakakinta, Birgediya Janar Tukur Gusau ya fitar, ta ce “muna bai wa al’ummar Najeriya tabbacin cewa rundunar tsaron Najeriya a shirye take ta samar da adalci da daidaito bisa dokokin ƙasa”.

Haka kuma Kwamitin sojin ruwa na majalisar wakilan Najeriya ya ce zai yi bincike dangane da zargin na Hussaina na zaluntar mijinta.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin, Yusuf Adamu Gagdi ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce “an tsare Seaman Abbas Haruna ne bisa umarnin wani babban soja. Saboda haka kwamitin zai bincika domin tabbatar da cewa duk waɗanda ke da hannu a al’amarin sun fuskanci hukunci daidai abin da suka aikata.”

Yusuf Gagdi ya ƙara da cewa “rashin imanin da aka nuna a kan sojan ruwan saboda ɗan saɓanin da aka samu tsakaninsa da babbansa ya sa mutane da dama sun zubar da hawaye a lokacin da mai ɗakinsa ke bayar da bahasin yadda a al’amarin ya faru.”

Za mu bi kadin lamarin – Ƙungiyar Amnesty

Daraktan Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta duniya Amnesty International a Najeriya, Isa Sanusi ya bayyana wa BBC cewa lamarin sojan ruwan akwai ɗaga hankali, “saboda zaluncin ya wuce misali.”

“Muna fatar jami’an da abun ya shafa za su ɗauki mataki su yi binciken gaskiya su gano abun da ya faru sannan a tabbatar da an yi adalci, duk wanda ya aikata ba daidai ba ya jefa wannan bawan Allah a cikin wannan hali da yake ciki da iyalinsa to a tabbatar an masa hukunci a tabbatar doka ta yi aiki domin zama izina.”

Ya ƙara da cewa tuni suka fara nazarin lamarin domin bin kadi domin tabbatar da adalci.

“Amma irin wannan lamari idan sun faru mukan tuntuɓi jami’an tsaron da abun ya shafa mu bayyana musu koken. Wasu lokutan mukan dace suna yin abun da ya kamata, wani lokacin kuma ba a yin nasara. Wannan ma za mu bi hanyoyin da muka saba domin tabbatar da an yi hukunci a kan waɗanda suke da hannu wajen zaluntar wannan bayan Allah.”

A game da ko yaya yake binciken zai kasance, ya ce, “Da yake batun ya ja hankalin ƴan Najeriya, ina kkyautata zaton za a yi adalci. Amma duk da haka ko da mutane sun manta mu ba za mu manta ba za mu cigaba da sa ido wajen ganin wannan magana ba ta mutu ba, ba a yi rufa-rufa ba in sha Allah ko shekaru nawa za a ɗauka.”

Yaya alaƙar manyan sojoji take da ƙanana?

An sha samun labarai masu ɗaga hankali na musayar yawo da ta rikiɗe zuwa tashin hankali tsakanin hafsoshin sojoji da ƙananan sojoji da ma sauran jami’an tsaro.

Haka kuma a gefe guda akwai zargin cewa sojojin sukan zalunci fararen hula idan suka gudanar da aikinsu.

A watannin baya ma an samu matsala tsakanin soja da wani ɗan kasuwa a rukunin shaguna na Banex da ke Unguwar Wuse 2 a Abuja.

Kafin sojojin su ɗauki wannan matakin, an ga wani bidiyo a kafofin sadarwa, inda a ciki aka ga wasu mutane sun far wa wasu sojoji, kafin ƴansanda suka shiga tsakani domin samun maslaha.

Haka kuma a tsakanin hafsoshin da ƙananan sojoji ana zargin akwai zaman tankiya a tsakaninsu.

Ana zargin kamar hafsoshin suna danne ƙananan sojojin, musamman ganin cewa yanayin aiki, na girmama na gaba.

A game da yadda alaƙar sojojin da manyansu, Isa Sanusi, ya ce sun daɗa suna samun koke-koke irin wannan.

A cewarsa, “Mukan samu koke-koke daga dukkan ɓangarorin jami’an tsaro masu ɗamara na irin zaluncin da suke fuskanta a cikin gida. Wannan ba sabon abu ba ne. Abun da yake faruwa shi ne tsarin shari’a da muke da shi a Najeriya yana da rauni.”

Mai fafutukar kare haƙƙin ɗan’adam ɗin ya ƙara da cewa akwai buƙatar hukumomi a Najeriya su fahimtar da manyan hafsoshin cewa ya kamata su zama misali mai kyau da nuna gaskiya da kula da ma’aikatansu.

“Ka da su rinƙa zalunci irin wannan, sannan kuma idan mutum ya yi laifi za a masa hukunci a masa hukunci daidai da laifinsa bisa ƙa’ida. Amma a ce an rufe mutum shekara shida wai saboda ya yi wani laifi ai wannan ya saɓa wa tunani ya saba wa hankali.”

BBCH

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *