Rundunar ƴan sandan babban birnin tarayya Abuja, ta ce ta kama mutum da shida waɗanda take zargi da sata da kuma lalata transfoma na bayar da hasken wutar lantarki.
Wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan sandan, SP Josephine Adeh ta fitar, ta ce ta kama mutanen ne a ranar Alhamis 11 ga watan Afrilun, 024 a Tipper Garage da ke anguwar Mpape.
Adeh ta ce an kama su ne lokacin da suke ƙoƙarin tserewa da wata transfoma wadda suka saka cikin wata motar ɗaukar kaya a Maitama, kuma cikinsu har da wani ma’aikacin kamfanin rarraba hasken lantarki na babban birnin tarayya.
Yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan mutanen,vkwamishinan ‘yan sanda na Abuja, CP Benneth C. Igweh, ya sake jaddada aniyarsa na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a al’umm a birnin.
Ya kuma buƙaci mazauna yankin da su yi taka tsan-tsan tare da yin amfani da layukan gaggawa na ‘yan sanda wajen bayar da rahoton abubuwan da ba su yarda da su ba.
- An gudanar da zanga-zangar neman sojojin Amurka da na sauran ƙasashe su fice Nijar
- Yan Sanda Na Binciken Yadda Wani Almajiri Ya fille Kan Karamin Yaro A Kano.