Ƴankasuwar Nijar sun yi watsi da ƙayyade farashin shinkafa

Spread the love

Ƴankasuwa a jamhuriyyar Nijar sun bijire wa dokar da ministan kasuwacin kasar ya sanya wa hannu da ke ƙayyade farashin shinkafa a fadin kasar.

Ƴankasuwar sun ce gwamnatin ta ɗauki matakin ne ba tare da yin shawara da su ba.

Dan haka suka ce yin biyayya ga wannan doka zai haifar musu da asara, ko ma ya janyo musu karyewar jari.

Shugaban ƴankasuwar Alhaji Sani Shekarau ya ce idan suka yi amfani da farashin gwamnatin za su iya durƙushewa.

Al’ummar ƙasar ne suka fara kokawa kan rashin biyayyar da ƴankasuwar suka yi ga dokar.

Gwamnan Gombe ya jinjina wa yarinyar da ta lashe gasar karatun Al-Ƙur’ani ta duniya

Abin da ministan kuɗin Najeriya ya ce kan zanga-zangar NLC

Ma’aikatar kasuwancin ta ce ta ɗauki matakin ƙayyade farashin shinkafar ne bayan ta yi la’akari da hauhawar farashinta da kuma irin wahalar da mutane ke sha.

Wasu mazauna Yamai babban birnin ƙasar sun ce babu irin shinkafar da aka ƙayyade mata farashin a kasuwanni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *