Rudunar ƴansandan Najeriya a jihar Anambra ta ce tana neman sufeta Audu Omadefu ruwa a jallo, kan zargin kisa a jihar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun ƴansanda a jihar, Ikenga Tochukwu, ya fitar a yau Talata ce ta sanar da hakan inda ta ce jami’in ya tsere tun bayan da ya aikata laifin da ake zargin shi da aikatawa.
An gurfanar da faston masu ‘azumin mutuwa’ bisa zargin kashe mutum 191
Muna son a yi sasanci kan ficewar kasashen Sahel daga Ecowas – Yan farar hula
Ta ce har yanzu ba a kai ga sanin inda ya ɓoye ba.
Haka kuma sanarwar ta nemi dukkan wanda ya gan shi ko ya san inda yake ya gaggauta sanar da ofishin ƴansanda mafi kusa.