Ƴansanda sun kama matar da ake zargi da jefa jaririnta cikin kogi

Spread the love

Rundunar ƴansanda a jihar Delta ta gabatar da mutum 30, wadanda ake zargi da aikata manyan laifuka ciki har da fashi da makami, da garkuwa da mutane da ƴan ƙungiyar asiri da kisan kai da sauransu.

Ƴansandan sun kuma ce sun samu nasarar ansar bindigogi 150 ciki har da AK-47 guda 32.

Kwamishinan ƴansanda a jihar, Abaniwonda Olufemi, ya bayyana haka a ranar Talata a yayin wani jawabi da ya yi wa ƴan jarida a shalkwatarsu da ke Asaba.

Ɗaya daga cikin laifukan da ya yi bayani a kai akwai na kisan wani jariri ɗan wata 10 wanda aka bayar da rahoton ɓatansa a ranar 4 ga watan Disamba, 2024.

“A lokacin da ake bincike, mahaifiyar yaron ta amsa cewa ita ce ta jefa yaron cikin rafi a ranar 31 ga watan Nuwamban 2024.

Ana ci gaba da tsare wadda ake zargin.

“An kama wadanda ake zargin a watannin da suka gabata, sai dai mun samu ƙalubale, amma an samu goyon bayan sauran jami’an tsaro, da masu ruwa da tsaki da kuma al’ummar Delta wajen dawo da zaman lafiya a yankin, ” in ji Abaniwonda Olufemi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *