Ɗalibar da ‘aka ci zalinta’ a makarantar Leads British na neman diyyar naira miliyan 500

Spread the love

Wata ɗaliba a Najeriya ta maka hukumomin makarantar Lead British a kotu bayan ɓullar wani bidiyo da ke nuna yadda ake ‘cin zalin ta’ ya yaɗu a intanet.

Lauyoyin Namitra Bwala sun ce makarantar ta Lead British da ke Abuja, babban birnin ƙasar ta gaza samar da ingataccen yanayin karatu.

Ta buƙaci makarantar da ta nemi afuwa a bayyane kuma ta biya ta diyyar naira miliyan 500, kwatankwacin dalar Amurka 350,000.

Bidiyon da ke nuna yadda wata ɗaliba ke zazzabga mata mari ya karaɗe shafukan sada zumunta a farkon wannan wata na Mayu.

Makarantar ta ce tana yin bincike kan lamarin kuma tana fatan ɗalibar za ta koma aji domin ci gaba da karatu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *