Ɗan gwamnan Jigawa ya rasu kwana guda bayan rasuwar mahaifiyarsa

Spread the love

Dan gidan gwamnan jihar Jigawa, Abdulwahab Umar Namadi, ya rasu kwana guda baya rasuwar mahaifiyar gwamnan.

Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan, Hamisu Mohammed Gumel ya fitar, ya ce marigayin mai shekara 24 ya rasu ne ranar Alhamis da maraice, sakamakon wani mummunan hatsarin mota a kan hanyar Dutse zuwa Kafin Hausa.

Marigayin na kan hanyarsa ne ta zuwa ta’aziyyar kakarsa – wadda ta rasu a ranar Laraba – lokacin da hatsarin motar ya rutsa da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *