Ɗan wake ya yi ajalin uwa da ’ya’yanta 5 a Kano

Spread the love

Wata mata da ‘ya’yanta biyar sun rasu gaba daya bayan da suka ci dan’wake, a kauyen Karkari da ke karamar hukumar Gwarzo a jihar Kano.

Wani makwabcin iyalan, Garba Muhammad ya sheda wa jaridar Daily Trust wadda ta ruwaito labarin, cewa, saboda fatar da talauci da kuma yunwa da iyalan gidan suke fama da su, matar wadda daman mijinta ya rasu, wadda kuma daman ita ke kula da ‘ya’yan nata biyar ta yi amfani da garin da ya lalace domin dafa musu dan’wake.

Jaridar Daily Trust ta riuwaito cewa lamarin ya faru ne ranar Alhamis, a gidan mijin matar, marigayi Malam Abdulkarin.

Mutumin ya ce, ”Cin wannan abinci ne ya yi sanadin mutuwar iyalan gidan su shida hadi da mahaifiyar.”

Wadanda suka rasun sun hada da, mahaifiyar mai suna Alhakatu Abdulkarim da ‘ya’yan nata biyar -; Bashir, da Firdausi, da Hafsat, da Usman da kuma Jamilu.

Kakakin rundunar ‘yansanda a jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce iyalan su shida da suka ci abincin aka garzaya da su babban asibitin Gwarzo, kuma a can likitoci suka tabbatar da rasuwarsu.

Sai dai ya ce, an fara gudanar da bincike domin tabbatr da ainahin abin da ya yi sanadin rasuwar tasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *